fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Dattijuwa Ƴar Shekara 77 Ta Sauke Al’qur’ani Mai Girma a Katsina

Malama Aishatu Nuhu, wadda ke aauna a Kofar Kaura, Kwalan-kwalan cikin garin Katsina, tayi saukar Al’qur’ani Mai Girma a ranar Asabar.

Daya Ddga cikin ƴaƴanta Aminu Dan Sarki ya shaida wa majiyarmu cewar, ta kwashe tsawon sahekaru goma sha biyu tana zuwa makarantar Malama Usaina Babba dake Daki Tara cikin garin Katsina har Allah ya sanya ta sauke yau.

Malama Aishatu Nuhu, tana da ƴaƴa da jikoki sama sa 90. Ƴaƴa da jikokin sun zo domin taya murnar samun nasarar sauke Al’qur’ani Mai Girma.

Allah ya albarkaci abinda ta karanto.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *