fbpx
Monday, October 25
Shadow

Direban bas da fasinjoji 18 sun tsallake rijiya da baya yayin da motar bas ta kifar da su a Jihar Ogun

Wani direban bas da fasinjojin sa sun yi tsallake rijiya da baya, bayan motar su ta yi hatsari a sanannen dogon gadar da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, jihar Ogun.

An ce motar tana tsakanin gudu sosai a lokacin lamarin ya faru a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba.

Sauran masu amfani da hanyar da suka ga hatsarin sun ruga zuwa wurin don taimakawa fasinjojin da suka makale a cikin motar.

An yi sa’a, dukkan fasinjojin 18 sun tsira da rayukansu, duk da cewa wasu sun samu raunuka.

Direban ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da tayar sa ta fashe ba zato ba tsammani yayin da yake gudu sosai, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kwamandan rundunar FRSC na jihar Ogun, Ahmed Umar, wanda ya tabbatar da hadarin, ya ce babu asarar rai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *