fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Dokar Hana Hawan Babura Da Dare: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 320 Da Suka Karya Dokar

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta kama wadanda suka karya dokar hana hawan babura daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe shidda na safiya har mutum dari ukku da ashiri a duk fadin jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina.
S P Gambo Isah ya kara da cewa rundunar ta kama mashina dari ukku da ashirin, ta gurfanar da mutane dari da tamanin da shidda a gaban kuliya, kuma an yanke masu hukunci. Su kuwa dari da talatin da hudu ana cigaba da bincike.
Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanyawa dokar hannu, wadda ta fara aiki a 20/1/2020. Domin magance matsalar tsaro a fadin jihar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *