fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Dole ne ka ba Gwamna Ikpeazu hakuri ko mu dauki kwakkwaran mataki a kanka – PDP ta fadawa sanata Adeyemi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, shiyyar Kudu Maso Gabas a ranar Litinin ta bukaci Sen, Smart Adeyemi da ya hanzarta ya nemi afuwa ga gwamnan jihar Abia, Dr. Okezie Ikpeazu game da kalaman batanci da yayi masa.

Sakataren yada labarai na shiyyar, Augustine Elochukwu wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai bayan taron kwamitin aiki na shiyyar, ya bayyana cewa babu kanshin gaskiya a cikin zargin da Sanata Adeyemi ya yiwa Gov Ikpeazu

Idan zaku tuna a makon da ya gabata Sanata Adeyemi yayi ikirarin cewa mashaya ne ke mulkin jihar Abia.

Sakamakon haka ne, Kwamitin Aiki na PDP, shiyyar Kudu Maso Gabas tayi kira ga Sanata Smart Adeyemi ya nemi afuwar Gwamna Ikpeazu a bainar jama’a, a cikin kwanaki 7, idan ba haka ba zata dauki kwakkwaran mataki a kan sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *