fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Dole ne ka mayar min da budurcina idan kana son mu rabu – Mata ta gayawa mijinta a gaban kotu

Wata mata ‘yar shekara 28, Toriola Suliat ta shaida wa mijinta, Toriola Lateef, cewa za ta amince da bukatar sa na a raba auren su ne kawai idan ya dawo da budurcin ta, kamar yadda ta kasance shekaru biyu da suka gabata kafin auren.

Suliat ta bayyana sharuddan ta a gaban wata kotun gargajiya ta Iseyin Grade C, inda mijin ya je neman a raba auren saboda tana yawan kunyatar da shi a gaban jama’a.

Ya fadawa Kotu cewa Suliat tana da dabi’ar ci masa mutunci a wurin aikinsa da kuma a gaban abokansa da danginsa.

Ya kara da cewa akai-akai yana nisanta kansa daga gidan saboda irin cin zarafin da take masa.

Saidai da take mayar da martani, Suliat ta ce Toriola bashi ne wanda take so da aure ba, kawai ta amince da aurensa saboda ya mata sihiri kasuwancinta ya bunkasa. Sai kawai ya bukaci gashin marar ta da kuma saduwa da ita

Tace hakan yasa ta amince aure sa, kuma kasuwancinta ya bunkasa sosai, amma yanzu lafiyata na ci gaba da tabarbarewa kuma yanzu ya fice daga gidan ya barta.

Ta kara da cewa dole ne ya mayar mata da budurcinta idan yana son mu rabu.

Da yake yanke hukunci kan lamarin, Shugaban Kotun, Cif Raheem Adelodun, ya ce za a dakatar da shari’ar har sai yanayin lafiyar Suliat ta inganta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *