fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

DSS ta gargadi sarakuna da malaman addinai da ‘yan siyasa su iya bakinsu

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya DSS, ta gargaɗi ƴan ƙasar ciki har da sarakunan gargajiya da ƴan siyasa da malaman addinai da cewa su guji yin duk wani abu da zai jawo saɓa doka da oda.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta PN Afunanya, DSS ta ce ta yi wannan gargaɗi ne don fahimtar da ta yi na yadda wasu mutane ke neman mulki ido a rufe da suke amfani da hanyoyin da ba su dace ba ta wajen tunzura ƴan ƙasa da kuma ruruta wutar siyasa.

Wannan sanarwa ta DSS ta zo ne a daidai lokacin da yanayin rashin tsaro ke ƙara ta’azzara musamman a arewacin Najeriya, inda mutane da dama ke nuna fushinsu kan abin da suke kira gazawar gwamnati wajen kasa magance matsalar.

Sanarwar ta ce: “Tuni masu irin wannan aƙida sun fara siyasantar da batun rashin tsaro a wasu sassan ƙasar bisa wasu dalilai na son kansu.

“Da yawansu suna amfani da damar yanayin da ake ciki don jawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƴan ƙasa, da neman suna da ko kuma sanya ƙasar cikin matsala.”

Ga dai saƙonnin da ke ƙunshe a cikin sanarwar kamar haka:

Hukumar ta gargaɗi dukkan masu hannu cikin irin waɗancan laifuka da ta ambata da su guji aikata su.

Ta kuma nemi ƴan siyasa da su yi komai bisa doka tare da gujewa maganganu ko ayyukan da za su iya kunna wutar rikici gabanin zaɓukan shekarar 2023.

“Masu saita tunanin al’umma kamar malamai da sarakunan gargajiya ma ana buƙatar su iya bakinsu su kuma guji kalaman tunzura mutane,” in ji saƙon.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *