fbpx
Thursday, December 2
Shadow

DSS ta kama mutum 48 bisa zargin satar jarrabawa a Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) sun kama mutum 48 bisa zargin hannu a satar jarrabawar shiga jami’a ta Joint Universities Preliminary Examinations Board (JUPEB).

Rahotanni sun ce hukumomin sun yi hadin gwiwa ne da ma’aiakatar ilimi ta kasar wajen kama mutanen.

Lamarin ya kai ga kama makaman jami’a da jami’an tsaro da ma’aikata da kuma dalibai a jihohi bakwai na kasar.

A kama mutanen ne a Jami’ar Wellspring, Benin, jihar Edo State; Jami’ar Christopher, Mowe, jihar Ogun da kuma Jami’ar Crown-Hill, Ilorin, jihar Kwara.

Kazalika jami’an tsaro sun kai samame a cibiyoyin da ake ba dalibai horo kan jarrabawar da ke jami’o’in McPherson da Precious Cornerstone da ke Ibadan da Ilara-Epe, a jihar Oyo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *