fbpx
Saturday, October 16
Shadow

DSS ta kama mutumin da yayi amfani da tsohon layin diyar shugaban kasa,Hanan Buhari

Hukumar ‘yansandan farin kata ta DSS ta kama wani mutum me suna Anthony Okolie bayan da aka sameshi da amfani da tsohon layin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari data daina amfani dashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Me shafin Sahara Reporters da DSS ta kama a kwanakin baya, Moyele Sowore ya bayyana cewa ya hadu da Okolie a tsarewar da DSS din ta mai kuma ya bayyanamai cewa an tsareshine tsawon makonni 10 saidai daga baya an sakeshininda aka bayyanamai cewa an yafemai laifin daya aikata.

Layin MTN ne Okolie ya siya, kamfanin na MTN ya sake saka lambar ta diyar shugaban kasar cikin wanda yake sayarwa bayan data jima bata yi amfani da ita ba, shi kuma Okolie sai ya siya wanda yace har yanzu yana da rasidin daya siya layin dashi.

Lauyan Okolie ya bayyanawa jaridar Vanguard cewa zasu je kotu inda zasu kai karar hukumar ta DSS da Hanan Buhari dan abi masa hakkinsa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *