fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Dubai ta dakatar da ƴan Najeriya daga shiga ƙasarta

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (Dubai) ta dakatar da jigilar fasinjojin jiragen sama daga Nijeriya zuwa ƙasar don shawo kan bazuwar cutar korona.

Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan kamfanin jiragen sama na Emirates ya dakatar da jigilar fasinjoji daga Najeriya har zuwa ƙarshen wannan wata.

Da yammacin ranar Alhamis ne kamfanin jiragen sama na Air Peace ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da wannan al’amari ga fasinjojinsa da ke zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Rahotanni sun ce matakin mai yiwuwa na da alaƙa da rashin jituwar da ƙasashen suka samu a kan tsarin Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa na yin wani gwajin nan take a filayen jiragen saman Nijeriya ga masu shirin zuwa ƙasarta saboda ba ta amince da takardun shaidar gwajin da ake yi a ƙasar ba.

Dubai na karɓar bakuncin dubban yan Najeriya da kan je don yawon shaƙatawa, ko da a watan da ya gabata hukumomin ƙasar sun tsawaita bizar masu yawon bude ido ciki har da na Najeriya da tsawon wata guda.

Qaddam Siddiq Isah, wani mai fashin baƙi ne kan al’amuran Gabas ta Tsakiya, kuma ɗan Najeriya da ke zaune a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ya shaida wa BBC cewa ”Ba shakka akwai rashin jituwa tsakanin hukumomin Najeriya da na Dubai a kan ɗaukar matakan kare kai daga cutar korona”.

Ya ƙara da cewa hukumomin Daular Larabawa na zargin cewa ƴan Najeriya na siyan takardar gwajin korona ta jabu, domin samun shiga ƙasar.

”Su hukumomin Najeriya suna ganin matakin da Dubai ta ɗauka a matsayin shishshigi a al’amuransu” a cewar Qaddam.

Akwai dai ƴan Najeriya da dama da ke shiga ƙasar da sunan kasuwanci bayan yawon shaƙawatawa, baya ga wasu da ke zuwa domin duba lafiyarsu.

Ta kai wasu ma kan je takanas don yin bikin aurensu a can, inda ko a shekarar 2019 ma an yi bikin biyu daga cikin mutanen da suka taba yin zaman dabaron wata uku a gidan Big Brother Nigeria, wato Bam Bam da Teddy A.

Hakan ne ya sa alaƙar ƙasashen biyu ta wannan fuska ake ganin take ƙara yauƙaƙa, kafin matakin da mahukunta suka ɗuka a yanzu.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *