Babban faston coci a Sokoto, Bishop Kuka ya bayyana cewa, duk da caccakar da yakewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari amma idan ya kirashi, yana daukar wayarsa.
Ya bayana hakane yayin ganawa da ‘yan jarida a Sokoto kan yawan caccakar da yakewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Kuka ya kara da cewa shi abinda ya fi caccakar gwamnati akai shine matsalar tsaro.
Yace kuma bai tsani shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba, abinda baiso shine kashe-kashe da nade-naden mukamai na rashin adalci.