fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Duk da hanun Amfani da Twitter, Gwamna El-Rufai yayi Amfani da ita, kuma Reno Omkri ya mayar da Martani

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi amfani da shafin Twitter wanda gwamnatin tarayya ta haramta amfani dashi.

 

Babban Lauyan gwamnati, Abubakar Malami ya bayyana cewa wanda har yanzu ke amfani da Twitter zasu fuskanci hukunci.

 

Saidai Gwamna El-Rufai yayi Amfani da Twitter inda ya rubuta cewa, Najeriya ya koyawa Kasar Amurka darasi kan yanda zata yi maganin manyan kamfanonin sadarwa masu kama karya.

 

Wannan rubutu na Gwamna El-Rufai ya jawo cece-kuce inda da yawa suka rika kiran a hukuntashi.

 

Cikin wanda suka yi wannan kira hadda hadimin Tsohon Shugaban kasa,  Goodluck Jonathan, watau Reno Omkri wanda yace kamata yayi dokar ta fara aiki akan Gwamna El-Rufai idan ba haka ba, Malami ya gaza.

 

“Based Nigeria: African country teaches US lesson in how to handle Big Tech tyranny,” the post to his over 1.9 million followers read.

 

 

“Dear @MalamiSAN, @elrufai tweeted this 20 minutes ago in violation of your #TwitterBan. If you do not start your arrest and prosecution with him, then you must admit that you are a failure and a man who does not keep to his word,” Mr Omokri wrote.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *