fbpx
Monday, November 29
Shadow

Duk da hukuncin kotun Koli, kada a kuskura a rantsar da wani gwamnan Bayelsa>>Gargadin Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC Adam Oshiomhole ya gargadi babban jojin jihar Bayelsa da kada ya kuskura ya rantsar da wani sabon gwamna a jihar Bayelsa.

Oshiomhole ya fadi haka ne jim kadan bayan dakatar da rantsar da gwamnan da kotun koli ta yi da umartar hukumar zabe ta janye shaidar zaman David Lyon na jam’iyyar APC zababben gwamnan jihar Bayelsa.
Idan ba a manta ba Kotun Koli ta tsige gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC a zamanta ranar Alhamis.
A hukuncin kotun wanda maishari’a Ejembi Eko ya karanta ya bayyana cewa duka Alkalai biyar da suka yi nazarin karar sun amince da wannan hukunci da kotun ta yanke.
Dalilin tsige sabon gwamnan Lyon David na jam’iyyar APC shine samun mataimakin sa Biobarakuma Degi-Eremienyo da laifin mika wa hukumar zabe takardun karatun sa na karya.
A dalilin haka Kotun ta bayyana cewa wannan matsala ta shafi gwamnan tunda shine ya mika a matsayin mataimakinsa a lokacin zaben gwamnan jihar.
Daga nan sai maishari’a Eko ya umarci hukumar ta bayyana wanda ya zo na biyu a zaben gwamnan jihar sannan a rantsar da shi ranar Juma’a.
Wannan hukunci na kotun koli ya yi wa jam’iyyar APC yanka baya domin hatta shugaban kasa ya shirya tsaf domin halartar bukin rantsar da sabon gwamnan jihar.
Jam’iyyar PDP ce ta zo na biyu a zaben inda ta samu kuri’u sama da 140,000 sannan kuma ta samu kuri’u akalla kashi 25 bisa 100 na kuri’un da aka jefa a kananan hukumomin jihar.
Sai dai kuma hakan bai yi wa jam’iyyar APC dadi ba inda shugaban ta Oshiomhole ya yi kira da kada a kuskura a rantsar da wani gwamna a jihar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *