fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Duk da ikirarin Iran na cewa ta kashe Sojojin Amurka 80: Shugaban Amurkar yace ba’a kashe musu kowa ba

Bayan harin rokoki da kasar Iran ta kai a sansanonin sojin kasar Amurka dake kasar Iraqi, Iran din ta yi ikirarin cewa, ta kashe sojojin Amurkar 80 inda tace wannan ramuwar gayyane ga kisan da kasar Amurkar ta wa sojanta, Qassem Soleimani.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Saidai a jawabin da yayi na bayan harin, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa harinbbai kashe kowa ba sannan kuma barnar da yayi bata taka kara ta karya ba. Saidai yace bayan harin da Iran din ta kai, kasar zata saduda.

Ya bayyana sabbin takunkumam tatgalin arziki dana hadahadar kudi da za’a sakawa Iran din.

Saidai ba kamar yanda yayi ta babatuba a baya cewa idan Iran din ta kaiwa Amurka Hari itama Amurkar zata kai mata harin ramuwar gayya mafi muni ba, Trump bai yi magana akan harin Ramuwar gayya na soji kan kasar ta Iran ba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *