fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Duk dan Siyasa zai so zama shugaban kasa>>Gwamna Fayemi

Gwamnan jihar Ekiti,  Kayedo Fayemi ya bayana cewa babu dan siyasar Najeriya da zai ki so a ce ya zama shugaban kasa.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channelstv a jiya Juma’a.

 

Gwamnan na amsa tambaya ne kan zabarsa da majalisar Jiharsa ta yi ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

 

Yayi dariya inda yace babu dan siyasar da ba zai so zama shugaban kasa ba idan ya samu damar hakan, duk da matsalolin da kasar ke fama dasu.

A baya, hutudole.com ya kawo muku yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace Najeriya ba zata sake fuskantar yakin basasa ba.

 

Saidai gwamnan ya ki bayar da tabbacin ko zai tsaya takarar shugaban kasar ko kuwa a’a inda yace a yanzu abinda ke gabansa shine kammala wa’adin mulkinsa a 2023.

 

“I am laughing. You know why? I get asked this question all the time. I don’t know any serious- minded politician who will have the opportunity to govern a country with the blessings that we have – in spite of the challenges – that will not give it a shot but we are not there yet.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *