fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Duk Labarai

Mijina Mugune, Naira 20 kacal yake bamu ni da yara idan zai fita>>Mata ta gayawa kotu

Mijina Mugune, Naira 20 kacal yake bamu ni da yara idan zai fita>>Mata ta gayawa kotu

Tsaro
Kotun dake Mapo Ibadan jihar Oyo, ta kashe aure tsakanin Alimat Onaolapo da mijinta, Biliamin saboda kasa rike gidansa da yayi.   Ta bayyanawa kotun cewa, mijin nata ya kasa kula da ita da yaransu 2. Tace kudin da yake bata na abinci basu taba wuce Naira 20 ba.   Matar tace yaran su biyu data haifa duka mininta bai kashe komai na kudin Asibiti ba, sai 'yan uwanta ne suka taimaka mata, tace shekaru shida bayan da ta aureshi, bata ci gaba ba a rayuwarta, tana nan inda take.   Dan hakane take neman a raba aurensu, Saidai mijin ya musanta ikirarin matar nasa inda yace  yana kula da ita kuma yana sonta har yanzu. Alkalin kotun, Ademola Odunade ya kashe auren inda yace mijin ya rika baiwa matar Dubu 10 duk wata dan kula da yaransu.
Budurwar ta hada bakibda saurayinta yayi garkuwa da ita dan su samu kudi

Budurwar ta hada bakibda saurayinta yayi garkuwa da ita dan su samu kudi

Uncategorized
'Yansanda a jihar Ekiti sun kama wata matashiya me shekaru 16, Abimbola Suluka da saurayinta, Oluwaseun Olajide bisa zargin yin garkuwa da mutane ta karya dan su nemi kudi.   Matashiyar ta hada baki da saurayin nata da kuma wasu abokansa 2 dan su saceta ta samu kudi.   Kakakin 'yansandan jihar, Sunday Abutu ya bayyana cewa, 'yar uwar yarinyar ce ta kai musu karar cewa, an sace 'yar uwarta.   Ya bayyana cewa sun nemi a basu 500,000 amma bayan da suka bayar da Asusun bankin da za'a zuba kudin a ciki, an gano me asusun inda kuma ya kai jami'an tsaron otal din da yarinyar da saurayinta suke.   Yatinyar tace tana son samun kudi ne dan ta gudu daga jihar saboda ita 'yar Fim take son zama amma Mahaifiyar ta tace sai ta zama Likita.
Da Duminsa: An gano manyan hanyoyi 2 da za’a wa Boko Haram illa a gama da ita baki daya

Da Duminsa: An gano manyan hanyoyi 2 da za’a wa Boko Haram illa a gama da ita baki daya

Tsaro
Mutuwar Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau ta yiwa 'yan Najeriya da yawa dadi ganin cewa shine jagoran kungiyar data addabi mutane musamman a Arewacin Najeriya da kashe-kashe.   Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ce ta kaiwa Shekau hari. Wanda hakan yasa ya kashe kansa maimakon ya yadda su kamashi.   Shugaban ISWAP, Abu Mus'ab Albarnawi ya bayyana cewa, Shekau ya zabi ya ji kungiyar lahira maimakon ta Duniya.   Hakanan ita kanta kungiyar Boko Haram,  Watau yaran Abubakar Shekau sun tabbatar da mutuwarsa inda suka nema masa gafarar Allah.   Wanda ya gaji Abubakar Shekau, Bakura Sahaba Modu dan shekaru 24 sannan bashi da kwarewa irin ta Abubakar Shekau.   Me sharhi akan ayyukan Boko Haram,  Bulama Bukarti ya bayyana cewa, w...
Amfanin kabewa a jikin Dan Adam da yadda ake sarrafata domin gyaran fata da sauransu

Amfanin kabewa a jikin Dan Adam da yadda ake sarrafata domin gyaran fata da sauransu

Kiwon Lafiya
Hanyoyi da ake amfani da kabewa ga rayuwar al’umma suna da yawan gaske musamman ma ga lafiyar jiki, domin Hausawa na cewa “abincinka maganinka”. To ita kabewa Allah ya yi mata baiwa da yawa da take taimakawa, a jiki dan’adam ya samu ingantacciyar lafiya. Kuma ga ita kabewar ba ta da wuyar samuwa haka ma wajen sarrafata babu wata wuya. Ana miya da ganyen ko ‘ya’yan kabewan. Ga dai wasu daga cikin amfaninta. · Gyaran fata: tana kare fata daga zafin ranar da ke wa fatar jikin mutum illa ya sa ta yi sumul-sumul. Da haka ne masana kiwon lafiya ke mata kirari da ‘mai maida tsohuwa yarinya’. · Tana taimaka wa masu ciwon cutar sikari: domin tana rage yawan ‘Glucose’ bayannan kuma ta kara masu yawan ‘Insulin’ da jiki ke samarwa. · Tana riga-kafin cutar daji: kamar yadda cibiyar bincike a kan cut...
Wasanni
Borussia Dortmund ta sakawa Manchester United wa'adin siyan tauraronta Jadon Sancho. Tun a kakar bara Manchester United ke harin siyan dan wasan, kuma yanzu manema labarai sun bayyana cewa United ta kara tayin da data yiwa dan wasan bayan Dortmund tayi burus da tayin farko. Shuwagabannin Manchester United nada yakinin cewa kungiyar zata siya dan wasan mai shekaru 21, duk da cewa Dortmund ta bukaci sama da fam miliyan 80 akan dan wasan. Manchester ta kammala yarjejeniya da Sancho akan kwantirakin shekaru biyar, amma manema labarai na Jamus Ruhr Nachrichten sun bayyana cewa Dortmund ta sakawa United wa'adin siyan Sancho nan da tsakiyar watan yuli.   Borussia Dortmund 'set Manchester United Jadon Sancho deadline' Borussia Dortmund have reportedly set Manchester United a dea...
Yanda Fusatattun matasan Yarbawa suka bankawa Motar Dangote data kade Mutane 2 wuta

Yanda Fusatattun matasan Yarbawa suka bankawa Motar Dangote data kade Mutane 2 wuta

Tsaro
Lamarin ya farune a karamar hukumar Yewa ta Arewa dake jihar Ogun, inda motar ta kade tare da kashe mutane 2.   Dalilin haka matasan yankin suka bankawa motar wuta, saidai direban ya samu ya tsere.   Kakakin hukumar kula da ababen hawa ta jihar, TRACE, Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin.   Kamfanin dillancin Labaran Najeriya,  NAN ya bayyana cewa, saids jami'an tsaro suka shiga dan kwantar da hankula.
Idan mutane suka ci gaba da bin Shuwagabannin da suka kasa samar musu da tsaro, addu’a ce kawai za’a musu>>Shehu Sani

Idan mutane suka ci gaba da bin Shuwagabannin da suka kasa samar musu da tsaro, addu’a ce kawai za’a musu>>Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa a yayin da mutane suka ci gaba da bin Shuwagabannin da suka kasa samar musu da tsaro da basu kariya, to Addu'a ce kawai za'a bisu da ita.   Sanata Sani ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta. https://twitter.com/ShehuSani/status/1406251264200130568?s=19 When people still worship the leaders who can’t protect their lives and provide for them,you can only pray for them.