
Na kadu da Mutuwar Shugaban Chadi, Munyi babban Rashi>>Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Yayin da yake bayyana kaɗuwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban giɓi a ƙoƙarin hadin gwiwa da ake yi na murƙushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da kaɗuwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ƙoƙarin da yake yi na kare kasarsa.’’
Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya.
"Sannan ya sanya...