fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Duk Labarai

Magidanci ya lalata rayuwar wata budurwashi da sunan zai aureta(zina har a cikin watan Azumi)

Magidanci ya lalata rayuwar wata budurwashi da sunan zai aureta(zina har a cikin watan Azumi)

Uncategorized
Wannan labarin wata yarinyace "yar shekaru ashirin da haihuwa, me ban takaici da ban haushi, ta wani fannin yana da ban tausayi, yarinyar ta aikawa me shafinnan na jarumane labarin abinda ya faru da ita, gadai takai taccen abinda labarin ya kunsa. Yarin yar tace ta gamu da wani mutumne(magidanci), yace yana sonta, a karin farko bata kulashiba, amma irin yanda yaketa mata maganar aure, sai hankalinta ya fara karkata kanshi har suka fara shakuwa, wata rana suna tare sai yaga wani hotonta a cikin wayarta, tana ninkaya a ruwa, sai yacemata aikuwa zaiso yaganta a zahiri tana ninkaya, ya mata tayin suje Mijibir Park, tacemai a'a, yayita rokonta, ta nuna bata yarda dashiba, kar yaje yayi lalata da ita, yayita mata rantsuwa da Allah babu abinda zai faru, har yake cemata, shimafa yana da 'ya...

Ana caca a kan Shugaba Buhari a Nigeria

Uncategorized
Wasu 'yan Najeriya sun soma yin caca a kan ranar da shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya shafe kusan wata uku yana jinya a birnin London, zai koma kasar. Wani shafin intanet da ke yin caca, NaijaBet.com, na tambayar mutanen da ke da sha'awar cacar su canki ranar da shugaban kasar, wanda ya fice daga Najeriya ranar bakwai ga watan Mayu, zai koma gida. A watan Yunin shekarar 2016 ne shugaban, mai shekara 74 a duniya, ya soma tafiya London domin yin jinyar abin da, a wancan lokacin, jami'an gwamnati suka bayyana da ciwon kunne. A farkon wannan shekarar ma Shugaba Buhari ya koma London inda aka duba lafiyarsa. A lokacin da ya koma kasar a watan Maris, ya ce an yi masa karin jini, ko da yake bai fadi larurar da yake fama da ita ba. Sai dai shugaban na Najeriya ya ce bai taba yi...
“Nafi ma’aikacin gwamnati samu da harkar fim”>>Hafsat Idris( Barauniya)

“Nafi ma’aikacin gwamnati samu da harkar fim”>>Hafsat Idris( Barauniya)

Uncategorized
Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi. Hafsa, wacce ake kira 'Barauniya' ko 'Yar Fim a Kannywood, tace ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza. Ta kara da cewa, "Yin fim ya fi aikin gwamnati domin kuwa abin da nake samu ma'aikacin gwamnati ba zai samu ba." Da fim nake yin hidimomina da na iyayena da na 'yan uwana," in ji jarumar. Ta kara da cewa ta koyi darasi da dama daga fim din "Barauniya" wanda shi ne na farko da ta fara yi a Kannywood. Na fahimci "yadda barayi ke sata da kuma yadda satar ke tagayyara wadanda aka yi wa". "Na nuna jarumta da rashin tausayi da dabaru irin na barayi," a cewar Hafsat. "A zahiri ni ba barauniya ba ...
“Buhari da kafiri zai tashi ranar kiyama, kuma zan iya kutuntumamai zagi ba abinda ya dameni”>>Ummi Zeezee

“Buhari da kafiri zai tashi ranar kiyama, kuma zan iya kutuntumamai zagi ba abinda ya dameni”>>Ummi Zeezee

Uncategorized
Jarumar fim din hausa, Ummi Zeezee ta saka wannan hoton na tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a shafinta na sada zumunta da muhawara, inda ta rubuta cewa shine gwarzonta kuma gwarzon dimokuradiyya a kasarnan, to saidai wannan abu ya jawo zazzafar muhawara tsakaninta da wasu mabiyanta, inda akayi musayar maganganu masu karfi, amma wadanda sukafi jan hankali sune, wani yayi kira ga Ummi cewa ta daine danganta kanta da Jonathan saboda ba musulmi bane kuma Allah zai iya tashinta dashi a ranar kiyama. Ummi ta mayarmishi martani da cewa to indai Allah zai tasheda Jonathan saboda tana sonshi to shima Buhari da Osinbajo Allah zai tasheshi tunda dai soyayyace tasa ya daukoshi ya bashi mataimaki...... Haka kuma Ummi sunyi musayar kalamai da wani wanda shima ta mayarmishi da martanin cewa...
Hotunan kamin biki masu kayatarwa na diyar Hauwa Maina, Maryam Abubakar

Hotunan kamin biki masu kayatarwa na diyar Hauwa Maina, Maryam Abubakar

Uncategorized
Diyar jarumar fim din hausa da turanci, Hauwa Maina, wato Maryam Abubakar kenan a wannan hoton na kamin biki ita da Angonta, Umar Ahmed wanda za'a daura aurensu kwannan idan Allah ya yarda, Hauwa maina tace zatayi matukar kewar diyartata, amma kuma a lokaci guda tana farinciki da samun siriki na gari. Muna musu fatan alheri. Wani abin birgewa da wadannan hotunan shine, basu taba jikin junaba kamar yanda aka saba gani a hotunan kamin biki na zamani.
Sani Maikatanga zai dauki mutane hotuna kyauta don murnar zagayowar ranar haihuwarshi

Sani Maikatanga zai dauki mutane hotuna kyauta don murnar zagayowar ranar haihuwarshi

Uncategorized
Shahararren me daukar hotonnan, Sani Maikatanga zaiyi murnar zagayowar ranar haihuwarshi ranar shabiyar ga watan Agustannan da muke ciki, idan Allah ya kaimu, kuma saboda murnar wannan rana, Sani yace duk wanda shima ranar haihuwarshi tayi daidai da wannan rana, kuma yana zaune a garin Kano, to yazo zai daukeshi hoto kyautar Allah wata'ala. To ga wadanda suke murnar zagayowar ranar haihuwarku sai ku shirya kuyi tururuwa shagon Sani.
Hotuna masu kayatarwa daga ziyarar da Osinbajo yakai jihar Kebbi

Hotuna masu kayatarwa daga ziyarar da Osinbajo yakai jihar Kebbi

Uncategorized
Ziyarar mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, zuwa jihar Kebbi tayi armashi sosai, Osinbajo hadu da gamayyar gwamnonin jamiyyar APC, a jiya, talata daya ga watan Agusta, inda suka hadu a Kebbin dan kaddamar da wani kata faren kamfanin sarrafa shinkafa da gwamnan jihar ya gida, yara 'yan makaranta da matasa masu bautar kasa, kai har dama jama'ar gari sun yiwa Osibajo kyakkyawar tarba. Wannan hoton na kasa, wata tarakatar nomace da akae kerata a jihar kebbi, wadda a jiya talata aka fito da ita tare da wasu kayan aikin gona da aka kera a jihar dan nunawa jama'a. Wannan hoton na kasa kuma Osinbajone yake duba wasu jibga-jibgan kifaye da aka kamo a argungu.