fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Duk matsalar tsaron da za’a samu bamu yadda a daga zabe ba>>Dattijon Yarbawa

Dattijon yankin Yarbawa kuma tsohon Sakatare Janar na kungiyar ma’aikatan Man fetur ta kasa, Cheif Frank Kokori yace basu yadda a yi amfani da matsalar tsaro wajan daga zabeba.

 

Ya bayyana hakane a hirarsa da Punchng, yace kuma babu maganar kauracewa zabe. Yace idan ka kauracewa zabe to shi wanda kake takara tare dashi, abin nasara ne a gareshi, dan zai lashe zaben.

 

Ya kuma bayyana takaici kan matsalar tsaro wadda yace tunda Najeriya take bata taba samun kanta a cikin irin wannan halin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *