fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Duk Sati Muna kona Tan 100 na lalatattun kudi>>CBN

Babban bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa a Duk Sati yakan kona kudin takarda da suka lalace da yawansu ya kai Ton 100 a guraren kona kudin da bankin ke da su guda 12 a fadin kasarnan.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bankin ya bayyana cewa doka ta bashi damar tattara da kuma kona kudaden daya gamsu cewa sun lalace ba za’a iya amfani dasu ba.

Sanarwar da bankin ta fitar tace saidai lura da yanda kone kudin ke taimakawa wajan gurbatar muhalli, bankin ya fara tunanin hada kai da kamfanoni masu zaman kansu da zasu iya amfani da takardun lalatattun kudin wajan yin wani abu na daban da zai amfanar da al’umma maimakon kodanu da ake yanzu.

Bankin yace yana gudanar da aikin kona kudinne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da suke basu tsatsauran tsaron daya kamata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *