fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Duk wanda ya min kazafin cewa na ci kudi, Allah ya isa ban yafe ba>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, yawanci ma’aikatan Gwamnati ne ke cinye Albashin jiha.

 

Yace amma sai a rika cewa, wai ‘yan siyasa ne ke cinye Albashin, irinsa da sauransu.

 

Yace amma duk wanda suka ce shine ke cinye kudin ma’aikata to Allah ya isa bai yafe ba, kuma sai Allah ya saka masa.

 

Yace har tashi yake da dare yayi Addu’ar duk wanda ya masa sharrin yana cinye kudin jihar Kaduna to Allah ya saka masa.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da ake yi dashi kai tsaye haka yanzu wadda wakilan hutudole.com suke bibiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *