fbpx
Friday, May 14
Shadow

EFCC ta cafke wasu mutane 14 da ake zargi da zamba ta hanyar intanet a Legas

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranar Talata ta ce ta cafke wasu mutane 14 da ake zargi da damfarar intanet a Legas
Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin sun hada da: Abiodun Gbolahan Seidu, Joseph Aganaga Ndubuisi, Sodimu Olawale Sikirudeen, Ohaekim Christopher, Ambali Oluwaseyi Rahman, Chibuzor Ebubedike, Salvador Abduljabar da Omohogbo Donald Ede.
Sauran sune: Thomas Obire Tobiloba, Olatunbosun Adeniyi Abiodun, Olugbemi Oluwatomigbeleke Eniola, Sanni Azeez Olayinka, Joseph Afenikhena Osaoman da Hamed Olayinka Olanrewaju.
Sanarwar ta kara da cewa, an cafke su ne a ranar Asabar 17 ga Afrilu, 2021 a Westwood Estate, Badore, Ajah Lagos, biyo bayan bayanan sirri da Hukumar ta samu game da zarginsu da hannu a zamba ta hanyar kwamfuta.
Kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da motoci, IPhone, na’urorin Android, kwamfutar tafi-da-gidanka na MacBook Pro da kayan kwala-kwalai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *