fbpx
Sunday, September 26
Shadow

EFCC ta kama tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura da matarshi bisa zargin rashawa

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama wani tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma sanata mai ci, Tanko Al-Makura da matarsa.

A halin yanzu jami’an na yaki da cin hanci da rashawa suna masu tambayoyi a hedikwatarta da ke Abuja, kamar yadda majiya daga hukumar ta EFCC ta shaida wa manema labarai.

Duk da cewa bayanai kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan da matar tasa ba su kammala ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, majiyoyin sun ce kamun nasu ya shafi cin amana da kuma karkatar da kudaden da ake zargin an tafka a lokacin mulkin tsohon gwamnan na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Mista Al-Makura ya yi gwamnan jihar Nasarawa tsakanin 2011 zuwa 2019 kafin a zabe shi a majalisar dattawa a matsayin sanata mai wakiltar gundumar sanata ta kudu ta kudu.

Lokacin da aka tuntubi kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya ce har yanzu ba a ba shi labarin yadda lamarin yake ba.

Lokacin da aka tuntube shi don yin tsokaci, kakakin tsohon gwamnan, Danjuma Joseph, ya ce ba shi da masaniya game da wadanda aka kama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *