fbpx
Sunday, September 19
Shadow

El-Rufa’i ya roƙi JAMB ta fasa rage wa ɗalibai maki

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce rage makin da hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a ta Najeriya JAMB ke yi ya mayar da ɗaliban arewacin kasar ragwaye.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Jridar The Cable ta rawaito gwamnan na cewa ko kadan rage makin ba ya taimaka wa yankin da ya jima yana fama da matsalar ilimi tun bayan samun ‘yancin cin gashin kai.

Ya shawarci hukumar ta fasa aiwatar da wannan shiri domin ba abun da zai haifar face sake jefa tsarin ilimin yankin cikin halin wani yanayi a cewarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *