fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

El Salvador ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta mayar da Bitcoin kuɗinta

El Salvador ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta mayar da Bitcoin kuɗinta.

Majalisar dokokin ƙasar ta amince da buƙatar Shugaba Nayib Bukele na mayar da kuɗin kirifto kuɗin ƙasar.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta kafa tarihi kuma matakin zai sauƙaƙa wa ƴan El Salvadore da ke zama a ƙasashen waje wurin aiko kuɗi gida.

Bitcoin zai zama kuɗin ƙasar tare da dalar Amurka nan da kwanaki 90.

Wannan sabuwar dokar na nufin dole ne duk wata sana’a ta amshi Bitcoin a matsayin kuɗi, sai dai idan ba ta da fasahar da ake buƙata a aika mata kuɗin na intanet.

Haka kuma ya ce matakin zai buɗawa kashi 70 cikin ɗari na ƴan ƙasar damar hada-hadar kasuwanci ko da ba su da asusun banki.

Tattalin arziƙin El Salvadore ya dogara ne kan yawan aika kuɗi da ake yi daga ƙasashen waje, wanda ya ƙunshi kusan kashi 20 cikin ɗari na gaba ɗaya kuɗin da ke shiga ƙasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *