fbpx
Monday, September 27
Shadow

Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa shugaba Buhari nba zai iya neman magani a Najeriya ba

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana dalilin da yasa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai iya neman magani a Najeriya ba.

 

Ya bayyana cewa, Shugaba Buhari ba zai iya ganin Likita a Najeriya ba saboda likitocin da suke kula dashi suna kasar Ingila ne.

 

Yace shugaban kasar ya kwashe shekaru 40 yana tare da wadancan likitoci dan hakane ma dole ya ci gaba da aiki tare dasu.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yake kare zuwan da shugaba Buhari yayi kasar Ingila dan ganin Likitocin sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *