fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Fadar shugaban kasa ta bayyana sunan kasar Larabawar da ake aikowa Boko Haram kudi

Abinda Muka Gano Game Da Boko Haram Da ‘Yan Bindiga, Zai Baiwa Kowa Mamaki, Cewar Shugaba Buhari

 

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ta gano dangatakar da ke tsakanin ta’addanci Boko Haram da kuma ta’adin da ‘yan bindiga masu satar mutane suke yi.

 

A cewar mai magana da bakin shugaban kasa, daga cikin masu taimaka wa wadannan miyagu akwai ‘yan canjin kudi da su ke da mutanen su a kasar ketare.

 

Malam Garba Shehu ya ci gaba da cewa akwai hujjojin da ke nuna ana aiko wa shugabannin kungiyar Boko Haram kudi daga kasar tarayyar Larabawa watau UAE.

 

Garba Shehu ya gaskata maganar da shugaban kungiyar gwamnoni, Dr. Kayode Fayemi, ya yi game da wadanda su ke da hannu wajen garkuwa da mutane.

 

Shehu ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan talabijin a ranar Talata.

 

Hadimin shugaban kasar ya ce abin mamaki ne ga kowane ‘dan Najeriya ace a wuraren ibada ake rufa asirin wadanda su ka kashe ‘yan sanda da jami’an tsaro.

 

A cewar Garba Shehu, tuni jami’ai sun yi bincike, kuma za a fara yin ram da wasu daga cikin wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a wannan danyen aiki.

 

Mai magana a madadin shugaban kasar ya ke cewa babu wanda za a rufa wa asiri idan gaskiya ta fito, ya ce ko da kuwa wadanda aka samu da laifin ‘yan siyasa ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *