fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Fadar shugaban kasa tace Zahara Buhari bata aiki da PPPRA

Fadar shugaban kasa ta karyata labarin Jaridar yanar gizo ta theSignalng.com da yace an dauki diyar shugaban kasa, Zahara Buhari aiki a ma’aikatar kula da farashin danyen albatkatun mai ta PPPRA yayin da aka kori wasu masu aikin wucin gadi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A jiyane Thesignal ta ruwaito labarin inda tace daya daga cikin ma’aikatan wucin gadinne ya bayyana mata haka.

Saidai a martanin da me magana da yawun uwargidan shugaban kasa, Aliyu Abdullahi ya fitar ta kan labarin yace Zahara Buhari bata aiki da hukumar ta PPPRA ko kuma ma wata hukumar gwamnatin tarayya inda yace wannan kirkirarren labarin karyane da aka yi da gangan dan batar da mutane.

Ya kara da cewa za’a dauki mataki kan lamarin.

Ya kara da cewa idan da sun san ba karya bane labarin, ya kamata ace sun yi tuntuba dan gano gaskiyar ikirarin na ma’aikacin wucin gadin.

Saidai a sabon Labarin da The Signal ta sabunta, tace wani daga cikin ma’aikatan na PPPRA ya bayyana mata cewa ba Zahara Buhari bace aka dauka aiki,dayar diyar shugaban kasarce, Hadiza Buhari Bello.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *