fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Falalar kwanaki 10 na tsakiyar watan Ramadan

Ramadana wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin daya da cikin shika-shikan Musulunci.

Wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu’o’i tare da neman gafara ga Mahalicci.

Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko na watan zuwa 10 na tsakiya da kuma kwanaki mafi daraja a 10 ta ƙarshe.

Shiekh Abubakar Baban Gwale ya yi wa BBC bayani kan falalar 10 ta tsakiya da kuma abubuwan da ake son Musulmi ya himmatu.

Malamin ya ce watan Azumi wata ne da ake ƙara alherin mumuni a cikinsa – duk lokacin da aka ƙara kwanaki alherinsa yana kara ƙaruwa.

“Manzon Allah (SAW) ya ce farkon watan Ramadan rahama ne, tsakiyarsa kuma gafara ce ƙarshensa kuma ‘yanta mutum ne daga wuta.”

Malamin ya ce idan aka shiga zango na gafara ba wai ana goge rahama ba ne – ana son mutum ya nunka ibada domin ya hada rahama da kuma gafara tare da kara kusanci ga Allah.

Ci gaban kwanakin Ramadan ƙarin samun falala ne da kuma kusantar dare mai albarka na Laylatul kadri.

Ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage

Shiekh Abubakar Baban Gwale ya bayyana ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage akansu kamar haka:

  • Musulmi ya dage da sallolin farilla da Allah ya wajabta a cikin jam’i.
  • Annabi ya kwaɗaitar da yin sallar Taraweeh da sallolin dare – Ramadan wata ne da Allah Y lizimta azumi a yininsa da kuma raya darensa.
  • “Akwai hadisin Abu Hurairah wanda Buhari da Musulim suka ruwaito cewa duk wanda ya tsaya ya yi sallah cikin dare a watan Ramadan yana mai imani da neman Lada za a gafarta masa zunubansa baki ɗaya da suka gabata.”
  • Ana son idan Musulmi ya yi Sallar Taraweeh bayan sallar Isha’i a cikin dare ya kuma dage ya raya dare. “Kuma duk abin da mutum ya haddace na Al Kur’ani ya kyautata niyya zai iya yin sallolinsa na dare da abin da ya sawwaƙa,” a cewar Shiekh Abubakar Baban Gwale.
  • Ana kuma son a ƙara dagewa da karatun Ƙur’ani.
  • Ana kuma son kara ƙoƙari wajen ciyarwa – kamar yadda ciyarwa take da falala a farkon Ramadan haka ma a 10 ta tsakiya domin karin samun falala da lada.
  • An kuma kwadaitar da yin kyauta sosai a watan Ramadan. Kyautar Manzon Allah tana bunƙasa idan Ramadan ya zo kuma kyautarsa yawanta ta fi iskar da ta ke ɗauke da girgije ta zubar da shi ba tare da rage komi ba.
  • Ana kuma son a dinga yafiya da tausasawa tun daga iyalai da ma’aikatan da ke karkashin mutum.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *