fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Falalar yin Sahur guda 7

Hakika cin abincin sahur sunnace mai girma daga cikin sunnonin Annabi s.a.w.
Manzon Allah ya kwadaita a gurare da dama akan yin sahur.
Wanda yayi sahur ya dace da lada mai girma da albarka kuma ya dace da sunnar annabi s.a.w. Wanda baiyiba bashi da laifi,amma yayi asarar lada mai yawa da albarka da kuma koyi da manzon Allah.
Kadan daga cikin Falalar Sahur;
1~YIN SAHUR ALBARKANE.
Annabi s.a.w yana cewa “kuyi sahur domin acikin Sahul akwai albarka”.
Bukari da Muslim.
2~ SAHUR KUMALLONE MAI ALBARKA
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
“Kuyi gaggawa zuwa ga Sahur kumallo mai Albarka”.
Abu Dauda da Nisa’I
3~SAHUR ALBARKACE ALLAH YA YIWA WANNAN AL’UMMA KYAUTARTA.
Manzon tsira s.a.w yake cewa:
Suhur wata albarkace Allah yayiwa wannan al’ummar kyautarta ita kadai, dan haka kada ku barta”.
NISA’I
4~KU NEMI ALBARKA ACIKIN SAHUR.
Annabi s.a.w yana cewa
“Ku nemi albarka acikin abu guda ukku;
-Cikin jama’a
-Da sammako
-Da Sahur “.
Dhabarany
5~ALLAH DA MALA’IKUNSA SUNAYIN SALATI GA MASU YIN SAHUR
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
“Lallai Allah da Mala’ikunsa sunayin Salati ga Masu sahur “.
Saheehul Jam’I
6~SAHUR YAKE BANBANTA TSAKANIN AZUMIN MUSULMI DANA AHLUL KITAAB.
Annabi s.a.w yace:
“Ku banbanta tsakanin azuminku dana yahudawa da nasara,tahanyar shan sahur “.
Muslim
7~KUYI SAHUR KO DA DA RUWANE DAN KADAN.
Manzo s.a.w yace:
“Kuyi Sahur koda da makwarwar ruwane”.
Saheehut Targheeb
Allah ka sadamu da albarkar sahur da falalar wannan wata mai alfarma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *