fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Farashin sufuri ya tashi da kashi 41 cikin 100 a biranen Najeriya – Hukumar Kididdiga ta Kasa

Hukumar Kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin kudin sufuri da matafiya ke biya a fadin Najeriya ya karu da kashi 40.56 cikin 100 tsakanin watan Satumban 2020 zuwa Satumba 2021.

Matsakaicin kudin sufurin da matafiya ke biya a watan Satumbar 2020 ya kasance N309.73, yayin da kuma farashin ya tafi N435.36 a watan Satumba, 2021.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na zirga-zirga na Satumba 2021.

Rahoton ya kara da cewa daga watan Agusta zuwa Satumba, matsakaicin kudin da matafiya ke biya na balaguron bas a manyan biranen kasar ya karu da kashi 1.11 cikin dari a duk wata.

Farashin ya tashi daga matsakaicin N430.58 a watan Agusta zuwa N435.36 a watan Satumba, a cewar NBS. Jihar Zamfara ta samu mafi yawan matsakaicin farashin bas a cikin gari kan N685.24 a cikin watan Satumba, sai kuma jihar Bauchi wacce ta samu matsakaicin kudin motar N630.17.

Jihar Taraba ita ce ta uku mafi girma a cikin rahoton inda farashin motar bas ya kai N560.73. A halin da ake ciki, Jihohin da suka fi kowacce saukin kudin bas, sun hada da Oyo mai matsakaicin farashin N215.43, Abia na da N245.07 sai Borno N300.45.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *