fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Farashin Waken Soya Zai Iya Hauhawa – Manoma Sun Yi Gargadi

Kungiyar manoman wake waken soya ta Najeriya (SOFAN) ta yi gargadin cewa ayyukan ‘yan bindinga a fadin kasar nan, musamman a Arewa maso Yamma, sun hana mambobin su noma waken soya a wannan kakar noman.

Shugaban SOFAN na kasa, Dakta Nafiu Abdu, ya shaida wa Aminiya cewa rashin tsaro, ambaliyar ruwa da jinkirin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi na cika alkawarin da ya yi wa manoma a lokacin da ya dace duk suna da jikin matsalolin da manoma ke fuskanta.

Ya ce farashin amfanin gona na iya hauhawa nan gaba kadan saboda wasu manoma har yanzu suna gwagwarmaya wajen noman, inda aikin da yakamata a yi shi cikin sa’o’i biyu, yana daukar kwanaki biyu ko sama da haka saboda wadannan matsalolin daban-daban.

Don haka kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo musu agaji a fannonin inganta kayayyakin aikin su na noma, isar da kayan aiki da wuri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *