fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Farfesa 2 ne aka sace a jami’ar Abuja>>ASUU

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya, ASUU ta bayyana cewa, Farfesa 2 ne aka sace daga jami’ar Abuja.

 

An samu cewa da misalin karfe 1 na daren da ya gabata ne ‘yan Bindiga suka shiga jami’ar suka sace malaman.

 

Kakakin ‘yansandan babban birnin tarayya,  Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.

 

Shugaban ASUU reshen jami’ar Abuja, Dr Kassim Umaru ya bayyana cewa, wanda aka sace din sune Professor Obansa da dansa da kuma Professor Oboscolo da dansa da diyarsa.

 

Sai kuma Sambo Mohammed da Dr Tobins. Yace suna kokarin ganin an sakosu sannan kuma ya nemi ‘yan Najeriya su sakasu a addu’a.

“Please, we need your prayers for their safe return,” the ASUU chairman said in a message.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *