fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Fasaha ce Zata Iya Fidda Najeriya Daga Kalubalan Da Ta Ke Fuskanta>>Auwal Ahmed Ibrahim Goronyo, Malami a Kaduna Polytechnic

“Ya kamata matasa su ba fasaha fifiko akan kwalin digiri” Ferfesa Idris Muhammad Bugaje, Bataran NBTE
Kowace kasa ta duniya tana laluben abun da yake fin zama a’alane kuma mafita agareta wajan gina al’ummar ta da saisaita arzikin ta.
Da yawa wasu jama’a kan Kali yawan mu; na ‘yan Najeriya a matsayin sila da jigon fadawar mu cikin kangin ni ‘ya sun da muke ciki: yawan jama’a rahamane kuma yana kawo cigaba indai har kasa tana da fadi da yalwa. A dalilin yawan mune da fadin kasar da muke da shi yasa muka daukaka a Afirika har yasa muke shigewa gaba a sahun daidaita wasu al’amura a fadin duniya. Amma idan aka zo fagen cigaba a sahun baya ake samun mu.
Najeriya kasa ce mai cike da albarka wadda ya kamata a ce ta wuce ajin da take tuntuni bayan kirkirarta a shekara ta 1914.
Kafin zuwan Turawa har bayan zuwan su an san kasar Najeriya da noma, iya tafiyar da mulki domin cigaban al’umma da kuma fasaha da kerekere. Domin kuwa kayan da Turawa suka same mu da su muna sawa aikin fasahar mune haka kayan da muke amfani da su wajan gina gidaje da yin noman wanda har waje muke fitar da su duk kirkirar mune. Amma, bayan samuwar man fetur mun yarda komi gami da riko da kayan aro da Bahaushe ke cewa abun banza ne wanda shine ya maida mu cima zaune kuma saniyar tatsa a fagen cigaba a duniya.
Dabi’un mu da sakacin mu wajan shabulatun-bangaro da muka yi da al’adun mu sune sun taimaka wajan samun kanmu cikin kakanikayin da muke ciki, ta haka muka zama ba wan ba wan karatun dan kama.
Samuwar man fetur a kasar nan ya kamata ya zama mabudine na bude alkairai da kasar nan take da su tinjim amma sai ya mai da gwamnatin mu da wasu masu taimakama cigaban kasar nan zaman dirshen da cin na bakagas domin a lokutanne aka dunga kama wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar nan da cin-hanci da rashawa, haka samun mai ne jigo na rabuwar kai da hadin kan ita giwar ta Afirika.
Hakazalika, ganin yadda ma’aikatan gwamnati ke kyelli da kyalkyalawa ya sa kowa ya maida hankalin sa zuwa ga karatun Boko domin samun abun duniya bayan ada karatun bayi da marasa galihu ne kawai suke yin sa.
Ada babu abun da ya kai malinta kima da haiba a matakan aikin gwamnati domin duk kusan jama’ar da suka ja ragamar samar da ‘yancin kasar Najeriya a shekara ta 1960 malamaine. Aikin ada kusan dolene domin ana son ciyar da kasa gaba amma sannu a hankali aka gujema aikin da hangen abun duniya a wasu guraban ayyuka.
Hakama, makarantun Kimiya da Fasahohi suna da karfi ada, dan ganin irin muhimmancin su wajan daukaka darajar kasa. Makarantu irin su Polytechnics, Colleges of Education da Technical Secondary Schools ada sai mai hazaka da basira yake iya samun shigar su. Kuma duk wanda ya gama karatu daga daya daga cikin wadannan makarantun baya zaman kashe wando domin tun kafin ya gama karatun ma’aikatu kan dunga kai goro-da-mari gami da kai farmaki da neman daliban su zama ma’aikatan su dan makarantun sune ke koyar da aiki a zahiri ba badini ba.
Sannu a hankali aka mai da Digiri abun alfahari kuma mafificin karatu a Najeriya wanda ya sa kusan kowane dalibai ko iyaye suka maida hankalin su ga karatun Digiri. Fifiko da muhimmanci da aka ba Digiri a Najeriya shi ya kawo saurin mutuwar masana’antun gwamnati da na ‘yan kasuwa da muke da su a kasar nan domin ya abun a faifai yake cewar ba a damu da kirkira ba sai karatun zube irin na aku. A yanzu a Najeriya, har kamfanin mai na kasa baya aikin ko ahu sai dai a tace man a wata kasa a kawo masa ya siyar. Haka, kamfanonin masaka da muke da su sun koma bololi inda wasun su kuma su ka koma shagunan siyar da kayan da aka yi a wasu kasashe.
Makarantun fasahar mu suna bukatar tallafi a daidai wannan lokaci da muke neman laluben mafitar neman tsira da tudun dafawa.
Farfesa Idris M. Bugaje shine sabon Sakataran ma’aikatar Fasaha ta Kasa wato National Board for Technical Education (NBTE). Farfesa Bugaje nada tabbacin cewar fasaha tafi kwalin Digiri. Bugaje na da yakinin cewar ilimin fasaha shine mafita ga yawan al’ummar da muke da su a kasar nan wadanda suka kusan kai miliyan dari uku. Domin yawan masu Digiri da kasar nan take da su da basu da aiki sun fi yawan shurin masaki dan kididdiga ta nuna sun fi miliyan hamsim.
Aikin gwamnati ya zama sai dan’wane da wane domin gwamnati baza ta iya ba kowa aiki ba. Haka kuma a yanzu tattalin arzikin kasar yana ruwa yana tangal-tangal da neman agaji, man fetur din da muka dora ran mu akan shi ya zama ruwan dare gama duniya kuma akwai hasashe na cewa nan da wasu shekaru man zai iya bacewa ko kuma a daina amfani da shi a duniya inda wani abu zai zama madadin sa.
Dole a sami mafita a cikin kowane kangi domin kasashen da muka sami ‘yancin kai tare da su a yanzu sun mana fintinkau. Kasar Indiya ita ce kasa ta biyu a yawan jama’a a duniya wadda a yanzu ta ke kokarin bin sahun kasar China (Sin) a fagen fasaha da kirkire-kirkire a duniya. Kasar Najeriya ita ce kasa ta shida a yawan jama’a amma yawan mu yana nema ya zama yawan dan kadanya.
Bincike ya nuna cewar yan Najeriya na daga sahun gaban kasashe a duniya sa suke zuwa kasar Indiya. Haka, binciken ya nuna cewar a cikin mutane 38,000 na jama’ar Najeriya da suke zuwa Indiya, mutum 18,000 neman magani suke zuwa a asibitocin kasar alhali muna da tarin likitocin da su kai fice a duniya, dan binbike ya nuna cewar sama da likitoci 20,000 ‘yan Najeriya ne suke aiki a kasashan waje.
Ba ma a yi maganar kasashen da kasar Najeriya ta samu ‘yancin kai a shekara daya da su ba kamar Madagascar, Benin, Congo da Somalia har wadanda ta riga su samun suna samun dagawa da cigaba fiye da Najeriya duk da kuwa basu da tarin arzikin kasa da na mutane kamar Najeriya. Kasar Singapore da ta sami ‘yancin kai a 1965 daga Malaysia ba za a iya saka ta a sahun Najeriya ba domin sama ta yima yaro nisa sabo da kasar ta rungumi fasaha da kirkire-kirkire. Haka sai ka duba yadda kasar Morocco ta ke kokari wajan daga darajar fasahar ta zaka gane fasaha ita ce silar dagawar kowace kasa.
“Fasaha ita ce abar da take tashe a fadin duniya” kamar yadda Farfesa M. Bugaje ya jaddada fasaha ita ce zinariyar da take walwali domin darajar ta.
Masu aikin Fasaha sun fi ma’aikatan gwamnati samun kudi da albashi mai tsoka a fadin kasashan da suka cigaba a duniya domin ko farfesoshi ba su kai su samun kudi ba. Dauka a wannan misalin a Najeriyance, Bakaniken da yake gyara mashina ko motoci guda biyar a duk rana kasan ya dara babban ma’aikacin gwamnatin da yake amsar albashi duk wata. Haka kuma zaka fahimci cewar ma’aikacin walda din da yake kera kofofi da tagogin gida ba ko kowane ma’aikacin gwamnati bane zai iya kafada da kafada da shi ba.
Kai ko aikin faci ba abun yardawa bane domin kuwa mai faci (balkanizer) yakan iya samun ninkinbaninkin din albashin karamin ma’aikaci na dubu talatin da gwamnatin Tarayya ta amince ma kananan ma’aikata wanda duk wata ake ta samun jani-in-jaka da jahohi wajan biyan kudin.
Aikin fasaha yana bayar da ‘yanci da sauki ga mai yin sa. Daliban da suka yi Polytechnics da Colleges of Education ba sai sun tsaya gwamnati ta basu aikin yi ba domin sun koyi komi da ake masu a makaranta kuma za su iya aiwatar da ayyukan a zahiri, inda ta haka ba za su iya rasa ayyukan yi ba.
A irin wannan lokaci da muke ciki na rashin zaman lafiya a kasar nan babu abun da zai samar da saukin wannan tashin tashina sai ba fasaha da kere-kere muhimmanci. Haka ya kamata a inganta makarantun koyon fasaha na kasar nan gami da inganta su. Hakazalika, akwai kasuwanni da suke koyar da fasaha domin samar da aikin yi. Irin wadannan kasuwannin kamar Kasuwar Fanteka ta Kaduna, Kasuwar Kofar Ruwa ta Kano da sauran kasuwannin gwamgwan ya kamata a basu kulawa da tallafi dan daga darajar kasar nan. Haka,  sai gwamnati ta cire kyashi wajan tallafama irin wadannan kasuwannin da ‘yan kasuwar wajan samar da wasu hanyoyin shigar kudi da samar da ayyuka dan magance matsalar tsaro.
Farfesa Idris Muhammad Bugaje lokacin da yake shugaban Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) ya tsamo sama da yara 300 daga unguwannin jihar Kaduna dan koya masu sana’o’in walda, kafinta, aikin gyaran magudanin ruwa da gini gami da samun kungiyoyin da suka tallafama daliban da kayan gudanar da sana’o’in bayan kammala karatun su. Har’ila yau, Bugaje ya shigo da shuwagabannin Kasuwar Fanteka cikin al’amuran da suka shafi fasaha da tallafama yaran da makarantar ta koyar. Dan cigaban Kasuwar Fanteka, Farfesa Bugaje ya daukaka darajar Kasuwar wajan samar da horo ga ‘yan kasuwar da daukaka basirar su wajan kere-kere da basu shaidar yin sana’o’in su bisa kwarewa a kowace kasa suka sa kafa.
Farfesa M. Bugaje Babban Sakataran, Ma’aikatar Fasaha ta Kasa (NBTE)  ya kabukaci dukkan makarantun fasaha na kasar nan wajan aiwatar da tsarin tallafama marasa aikin yi da wadanda suka bar makarantu gami da basu kayan sana’o’i kamar irin wanda wanda ya aiwatar a Kaduna Polytechnic. Tabbas tsarin zai taimaka gaya wajan aza kasar nan a kan tubalin da sauran kasashe suka bi wajan inganta kasashen su. Amma fa sai gwamnatin Najeriya da jihohi sun marama wannan kudiri baya za a samu alfanun sa.
A Najeriya a yanzu muna da makarantun polytechnics guda 44 ne a inda muke da jami’o’i (university) guda 170 wanda yake nuna dole sai an yima hanci tubka. Sannan matsalar banbanci tsakanin mai kwalin Digiri da na masu karatun fasaha shine silar yin shabalatin bangaro da fasaha a kasar nan. So samu, mai kwalin fasaha ko aikin fasaha ya kamata ya zama mafi amsar albashi mai tsoka a duk guraben ayyuka a kasar nan kamar yadda yake a kasashen da suka cigaba a doron duniya.
Haka su ma jama’a, ya kamata su gane karatun fasaha yafi karatun Digiri kawo kudi sannan kuma shine karatun da yake cicciba kasa sama gami da magance talauci da fatara. Ya kamata kowane mai karatun fasaha da aikin fasaha ya dunga ganin kansa kamar sarki. Kar ya dunga kallon aikin ofis a matsayin wani babban al’amari domin kuwa duk wannan kyale-kyalan duk hangen dalane tamkar kitsan rogo, dan ko yankan rake kake ka sani firarta fasaha ce haka kwasan bola sana’a ce abar alfahari kuma wadda ke hana bara da roko haka akwai wadanda suke cikin tarin daula a cikin irin wadannan sana’o’i. Abu mafi a’ala shine kowa ya inganta sana’ar sa, a zamantar da ita, a kawo mata tsari gami da neman ilmi da zurfafa bincike dan samun riba mai yawa.
Idan muka rike fasaha mutuka sai muma an fara biyo mu har kasar mu. Riko da fasaha ita ce zata magance malalar Turawa zuwa cikin kasar nan domin yimana aikace aikace. Yanzu kalli yadda Turawa ‘yan kwangila suke zuwa suke mana ayyuka a cikin kasar mu kuma in ka duba zakaga masu ayyukan wahalar duk jama’ar kasar mu ce sai dai, aikin Turawan shine sa ido da jan ragamar ayyukan.
Sana’ar hannu jari ce koda kuwa sana’ar bola ce domin sana’ar hannu ita ce sana’ar da akema taken tafi da gidan ka wanda ko ina za ka kana tare da abar ka kuma gashi bata da tarin wahalhalu haka bata da wahalar samu in dai mutum ya iya.
Ko shakka babu kamar yadda wasu kasashe suka kubuta daga kangin talauci, Najeriya na dab da samun kubuta wajan samun cigaba mai daurewa idan dukkanin mu muka yarda cewar Najeriya ita ce kasar mu kuma ba mu da kasar da ta fita. Haka kuma samun Digiri baya nufin mai Digiri ya fi kowa a rayuwa domin samun abun dogaro da kai shine yafi komi. Masu sana’o’in hannu suna taimakawa gaya wajan cigaban kasa domin zai yi wuya kaga mai aikinn hannun da ya kware a sana’ar sa da bashi da yara wadanda suke samu daga gare shi kafin ya yaye su. Ko shakka babu kasar nan zata fi kyau idan kowa daga ministoci da gwamnoni da talakawa har shugaban kasa ya zamana mun koyi wata sana’ar hannu ko dan taimakama kan mu da kan mu a gidajen mu dan wannan zai karfafama masu sana’o’in hannu da sa su su dunga samun karfin gwiwa a tafiyar da sana’o’in su.
Auwal Ahmed Ibrahim (Goronyo)
Malami a Kwalejin Kimiya da Fasaha, Kaduna (Kaduna Polytechnic)
Sashen koyar da aikin jarida
Za a iya tuntubar Goronyo ta Emel: [email protected]

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *