fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Fasinjoji 8 sun mutu yayin da babbar mota ta fadi a wata gada a Osun

Mutane 8 aka tabbatar da mutuwarsu a hatsarin babbar motar da ta faru a ranar 27 ga wata gada, a Osogbo, Jihar Osun, safiyar Asabar.

Hatsarin wanda ya yi sanadin mutuwar ya faru ne da misalin karfe 1:20 na safiyar Asabar.
Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa motar Volvo FL7 mai lamba KMC 35 ZJ na haye gada ne lokacin da direban ya rasa sarrafa motar saboda yawan lodi.
Motar wacce ke dauke da manja da guru zuwa arewa na dauke da fasinjoji 61 tare da direban.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Osun, Kudirat Ibrahim, wacce ke wajen da hatsarin ya faru ta shaida wa manema labarai cewa an kai fasinjojin da suka samu rauni asibitin koyarwa na jihar Osun da Asibisro da ke Osogbo.
Ta ce “motar wacce ke dauke da lodi mai dauke da kaya da fasinjoji sama da 60 na kokarin haurawa amma sai ta fara dawowa ta baya baya. Ta fadi ne a gefe a cikin magudanar ruwa, tana zubar da jarkokin manja kan fasinjojin kuma ta kashe wasu a cikinsu. ”
Ta kara da cewa an kai wadanda suka mutu dakin adana gawa.
Ta yi kira ga masu amfani da hanya da su kasance masu lura a koyaushe kuma su bi dokokin hanya don kauce wa afkawa cikin hadurran da ka iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *