fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Fim din Rahama Sadau na Mati a Zazzau ya kafa sabon Tarihi a Kannywood

Fim din Mati A Zazzau na tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ya dauki hankula sosai saboda irin karbuwar daya samu a wajan jama’a musamman A Ranar Farko da aka fara nunashi a Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ya kafa tarihin zama fim din Hausa na farko daya fi daukar hankali da kawo kudi a ranar farko ta nunashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ranar Juma’ar data gabatane aka fara nuna fim din inda saida aka fasa nuna wani fim din Turanci saboda karbuwar da Mati a Zazzau ya samu

Bidiyo da suka rika yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yanda matasa suka rika turmitsutsu wajan Shiga kallon fim din a Ranar Farko.

Fim ne da ya kunshi Barkwanci, Fada akan Gado, Auren Dole da kwadayi, kamar yanda Rahama Sadau ta bayyana.

Wani abin karin daukar hankali a fim din shine yanda Mawakiyarnan Afro Dija ta fito a fim din, sauran manyan jarumai a fim din sun hada da Ali Nuhu, Adam A. Zango, Rahama Sadau, Sadiq Sani Sadiq, Jamila Nagudu, Rabiu Rikadawa, Umar Gombe, Zaharadeen Sani dadai sauransu.

Tuni manyan jarumai suka fara tururuwa wajan zuwa kallon fim din.

Mati A Zazzau ya samu yabo daga Fadar shugaban kasa da fadar Gwamnatin jihar Kano

Tun kamin fitowar fim din  a lokacin da Rahama Sadau ke tallatashi, hadimin shugaban kasa kan sabbin kakafen sadarwa, Bashir Ahmad ya yaba da fim din inda yace, Da Alama duka manyan taurarin fina-finan Hausa hadda sabiwar tauraruwa, Dija na cikin wannan fim na Mati A Zazzau, ina daya daga cikin masu son kallon wannan shirin.

Shima hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya yaba da wannan fim inda ya bayyana son ganinshi.

Labarin fim din ya daukin hankula sau fiye da Miliyan 17 a shafin Twitter.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *