fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Fitaccen Shugaban Fulani, Sale Bayari Ya Rasu

Wani fitaccen shugaban Fulani, mai kishin kasa da kuma tsohon dan jarida, Sale Bayari ya rasu.

Bayari ya rasu a daren Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), bayan gajeruwar rashin lafiya.
Har zuwa rasuwarsa, ya kasance Shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria (GAFDAN) da kuma tsohon sakatare na kasa na kungiyar Miyetti Allah (MACBAN), inda ya yi aiki na kimanin shekaru 20.
Ya kuma shiga cikin shirye-shiryen ci gaban kasa da dama, kuma ya kasance mai ba da gudummawa ta wannan fuska, a tsakanin sauran ayyukan ci gaban al’umma.
Shugaban GAFDAN na Jihar Filato, Garba Abdullahi Muhammad, ya tabbatar da rasuwar Bayari ga Aminiya.
An binne Bayari da safiyar Juma’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *