fbpx
Monday, November 29
Shadow

Fulani makiyaya da yan bindiga suke wa aiki – Kungiyar MASSOB ta caccaki kungiyar hadin kan Arewa da suka ce kada Shugaba Buhari ya saki Nnamdi Kanu

Kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra (MASSOB) ta caccaki kungiyar hadin kan Arewa (CNG) bisa sukar shugabannin kabilar Igbo kan ziyarar da suka kai wa shugaba Buhari da kuma rokonsa da ya saki jagoran ‘yan asalin Biafra (Nnamdi Kanu) ba tare da wani sharadi ba.

Ministan sufurin jiragen sama na Jamhuriyyar farko, Cif Mbazuruike Amaechi a makon jiya Juma’a ya jagoranci dattawan yankin Kudu maso Gabas suka ziyarci shugaban kasar a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa inda suka bukaci a yi wa Kanu da sauran matasan kabilar Ibo da ake tsare da su afuwa.

Sai dai gamayyar kungiyoyin Arewa sun nemi shugaban kasar da kada ya saurari bukatar ‘yan kabilar Igbo inda suka ce jinin ‘yan Arewa zai rataya a kan Buhari idan ya saki Nnamdi Kanu.

Saidai a cikin nata martabin kungiyar MASSOB tace, Kungiyar Hadin Kan Arewa bata son shi gaban kasar nan shi yasa take son a cigaba da tsare Kanu da sauran mambobinta, ta kara da cewa hakan ya nuna kungiyar tana yiwa Fulani makiyaya, Yan bindiga da Boko Haram aiki ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *