fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Fursunonin kurkukun Ikoyi 20 za su zana jarrabawar UTME

Fursunoni 20 dake tsare a kurkukun Ikoyi sun nuna sha’awar zana jarabawar samun gurbin shiga manyan makarantun gaba da sakandare wato UTME ta 2021.

Sanarwa ta fito ne daga bakin Mista Rotimi Oladokun, mai magana da yawun Hukumar Kula da Fursunonin Najeriya a jihar Legas ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa fursunonin za su kasance cikin shiri tsaf domin zana jarabawar.

Kakakin na NCoS ya kuma lura da cewa, karin fursunonin sun nuna sha’awar ci gaba da karatunsu, kasancewar sun bi sauye-sauye da dama.

Oladokun ya kara da cewa a shekarar da ta gabata, wani fursuna mai shekaru 60 yana cikin wasu mutane 25 da suka zana jarabawar UTME ta 2020 a cibiyar gyara.

Ya kuma ce sabon wurin, inda fursunoni za su zana jarabawar, an tsara shi ya kai kashi 80 cikin dari kuma an kammala shirya kwamfutoci da sauran abubuwan da ake bukata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *