fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ganduje baya cika alkawari, Shekarau kada ka yadda da shi>>Muazu Magaji

Tsohon Kwamishinan kula da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano Mu’azu Magaji Dan Sarauniya, ya gargadi tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da kada ya kuskura ya karbi tayin sulhu da Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, domin a cewarsa Gandujen baya cika alkawari.

Muazu Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, ko a baya Gwamna Ganduje ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau alkawari amma bai cika masa, dan haka yake gargadinsa da kada ya kuskura ya karbi duk wani tayin sulhu da Gwamna domin ba mai cika alkawari bane.

Yaya kuke kallon wannan dambarwa?

Daga Daily Nigerian

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *