fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ganduje Ya Ba da Gudummawar Naira Miliyan 20 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kasuwar Katsina

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ba da gudummawar naira miliyan 20 ga wadanda gobarar kasuwar Katsina ta shafa.
Ganduje ya ce za a yi amfani da kudaden ne don rage wahalhalun da wadanda abin ya shafa suka fuskanta.
Shi ma a ranar Talata ya gabatar da wasikar ta’aziya ga Gwamnan Jihar, Aminu Masari, yana yaba masa saboda kafa kwamiti mai karfi don gano ainihin musabbabin mummunan tashin hankalin.
Ya kara da cewa ko shakka babu abin takaici ne matuka ganin yadda lamarin bai shafi harkokin kasuwanci da jama’ar jihar Katsina ba kawai, har ma da mutanen arewacin kasar.
A nasa bangaren, gwamna Aminu Masari ya godewa gwamna Abdullahi Ganduje bisa wannan tallafi wanda ya yi imanin zai taimaka kwarai da gaske wajan taimakawa ‘yan kasuwar wajen gyara wani bangare na abin da suka rasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *