fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Garuruwan Najeriya da suka aje Azumi, ake Sallah a Yau

Duk da yake me Alfarma Sarkin Musulmi,  Muhammad Sa’ad Abubakar na III yace a cika Azumi 30 saboda ba’a ga watan Shawwal ba, wasu dai basu bi wannan Umar ni ba.

 

Anan mun tattaro muku garuruwan da aka sha ruwa, za’a yi Sallar Idi a yau, Laraba.

 

Za A Gudanar Da Sallar Idi A Garin Jega Dake Jihar Kebbi A Yau Laraba

Bayan tabbatar da ganin wata a wasu sassa a Nijeriya da kuma makwabtan ta Niger, har ma a karamar hukumar Jega, wasu musulmai a yankin sun sanar cewa za su gabatar da sallar Eidi a yau Laraba, da misalin karfe 9:00 na safe.

Za a gudanar da sallar neI a Masallacin Eidi dake kusa ga Makarantar bokon Birnin Yari dake garin Jega, jihar Kebbi.

 

Ƴan Shi’a Almajiran Sheik Zakzaky Ma Za Su Yi Sallah A Yau Laraba Domin Suna Da Tabbacin Ganin Wata A Sokoto Da Wasu Wurare Na Sassan Nijeriya

Daga Bilya Hamza Dass

Mabiya Shi’a a Nijeriya sun bayyana cewa sun ga watan Shawwal a garin Sokoto, Lafiya da wasu wurare, inda suka ce yau Laraba ne zai zama 1 ga watan Shawwal, dan haka za su sallace a yau.

Wakilin Sheikh Zakzaky na garin Zariya, Malam Abdulhameed Bello, ya bada sanarwan misalin ƙarfe 9 da minti 57 na daren jiya Talata, inda yace; “Muna farin cikin sanar da Ƴan uwa cewa mun samu labarin ganin watan Shawwal daga yankunan Sakkwato, Yawuri, Lafiya, Nijar da sauran wurare.

“Tare da wasu sassa na ƙasar nan. Mun samu ƙarfin guiwan cewa; tabbacin ganin watan dan haka gobe Laraba zai zama 1 ga watan Shawwal 1442H Insha Allah” in ji shi.

 

WATA SABUWA: Allah Ne Kadai Zai Hana Ni Ajiye Azumi A Gobe Laraba, Saboda Ita Ce Daya Ga Watan Shawwal, Cewar Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, Sokoto

YANZU-YANZU: Mabiya Darikar Tijjaniyya A Nijeriya Za Su Yi Sallah A Gobe Laraba Bayan Sheik Dahiru Bauchi Ya Sanar Da Ganin Jinjirin Watan Shawwal

Shehin Malamin ya bayyana cewa an ga watan ne a Azare, Bauchi da Gombe, don haka a gobe zai gudanar da sallar idi.

Rahotannin Sun fito ne daga Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

2 Comments

  • Lauwali manchester kamba

    Dai daita kan musulmi a najeriya sai dai Allah daya halicce mu,
    Ya Allah ka hada muna kawunan musulmin najeriya 🤲

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *