fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Gayawa mutane cewa su dauki makamai su kare kansu ya nuna cewa baka cancanci zama shugaba ba>>CSO ta gayawa Masari

Kungiyar dake ikirarin kare hakkin bil’adama ta CSO ta caccaki gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masarki kan kiran mutane su tashi su kare kansu daga ‘yan Bindiga.

 

Daraktan kungiyar, Ariyo Dare ne ya bayyana haka inda yace Masari zagaye-zagaye yake, baya son fitowa karara ya fadi gaskiya cewa, shugaba Buhari ya gaza.

 

Kungiyar tace bai kamata a fara kiran mutane su dauki makami ba tunda ba’a kure dukkan matakan da ya dace ba wajan ganin an samar da tsaro.

 

Tace misali ‘yansandan jihohi da ake son samarwa wani mataki ne da ake ganin zai taimaka wajan kawo karshen matsalar tsaron.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *