fbpx
Saturday, July 24
Shadow

Gbajabiamila Yayi Kira Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya Tare Da Cigaban Kasa, Yayin Da Yake Taya Musulmai Murnar Maulidi

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a ranar Alhamis ya yi kira ga Musulmai da sauran ‘yan Nijeriya da su kara nuna kaunar juna tare da yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaban kasar.
Gbajabiamila ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Lanre Lasisi, ya fitar a ranar bikin maulidin Annabi Muhammad (SAW) na wannan shekarar.
Ya taya Musulmin duniya murna, sannan ya ce halaye da koyarwar Manzon Allah su zama abin kallo ga kowa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *