fbpx
Monday, November 29
Shadow

Gobara ta hallaka yara ‘yan makaranta fiye da 20 a Maradi ta Nijar

Gwamnati ta rufe makarantu a jamhuriyyar Nijar tare da ƙaddamar da zaman makoki na tsawon kwanaki uku a birnin Maradi, sakamakon aukuwar wata gobara da ta tashi a wata makarantar renon yara da firamare, wadda ta yi sanadin mutuwar yara ƙanana fiye da ashirin.

Kazalika wasu yaran kusan ashirin kuma sun gamu da mummunar ƙuna a lamarin da ya faru ranar Litinin da safe.

Hakan dai ya auku ne yayin da ake ta ƙoƙarin zakulo mutanen da ake zargin sun maƙale a wani waje da ake hakar gwal a yankin jihar ta Maradi.

Babban daraktan kula da ilimi a jihar Katsinar Maradi ne ya bayar da sanarwar rufe makarantun, da kuma zaman makokin na tsawon kwanaki uku, daga gobe Talata zuwa Alhamis, a iya fadin garin Maradi, babban birnin jihar.

Gobarar ta tashi a safiyar Litinin a makarantar renon yara da firamare ta AFN ta kungiyar mata a garin a unguwar Sabon Gari, kusa da babban filin kwallo na garin Maradin.

Saminou Salisou Rijiyar Lemo, wani dan jarida mazaunin garin na Maradi, ya yi karin bayani kan aukuwar wannan al’amari inda ya ce abin ya yi muni sosai.

“Iyaye maza da mata sun cika asibitin suna ta koke-koke suna cikin mawuyacin hali. Wasu iyayen ma da suka je asibitin ba su ga ƴaƴan nasu ba, don da yawa ba a ma gane fuskokinsu saboda ƙonewar da suka yi.

“An samu wutar ta mutu tun misalin ƙarfe ɗaya na rana, to amma ana ta ɗibar gawarwakin mutane ana tafiya da su asibiti.”

“Zuwa yanzu dai likita ya ce akwai kusan mutum 22 da suka mutu, sannan da wasu 17 suna karɓar magani,” in ji shi.

Saminou Salisou ya ce gwamnan jihar ya je wajen kuma ya yi wa iyayen yara jawabin kwantar da hankali tare da yi musu alkawarin yin duk abin da ya dace don ceto waɗanda suka jikkata.

Sai dai ya ce har yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba. “Kusan mutum 250 ne a makarantar kuma ajujuwan na zana ne.,” in ji ɗan jaridar.

Wannan gobara ta auka ne yayin da ake ƙoƙari ceton mutanen da riftawar wani rami ta rutaa da su a wani waje da ake haƙar gwal a garin Dan Isa na yankin jihar Katsinar Maradin, inda rahotanni ke cewa ya zuwa yanzu mutum fiye da 30 sun rasa rayukansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *