fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Gobara ta kone dakin ajiye bayanai na hukumar zabe, INEC a jihar Kano

Wata gobara da ta tashi ta kone wasu sassan ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano.

Lamarin gobarar, wanda ya faru da misalin karfe 9:30 na safe a Cibiyar Gudanar da Bayanai na ofishin INEC, ya kone kwamfutocin tafi-da-gidanka, kwamfutoci da dukkan ginin, in ji jaridar Daily Trust.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa ma’aikatan kashe gobara na Tarayya da na jihar Kano ne suka kashe wutar.
“Sun iso ne kimanin minti 20 bayan barkewar gobarar.
“Duk da cewa jinkirin da aka samu ya kara wa wutar wuta ta kona kusan dukkanin ginin amma sun iya shawo kan lamarin.”
Wasu daga cikin ma’aikatan wadanda abin ya faru a gaban su, sun lura cewa gobarar ta fara ne biyo bayan canjin wutan lantarki wanda hakan ya haifar da fashewar wasu na’urar sanyaya daki a cibiyar.
“A cikin cibiyar bayanan akwai kwamfyutocin tafi-da-gidanka, batura da sauran kayan aiki masu alaka da su don ayyukan sarrafa bayanai,” in ji daya daga cikinsu.
Sun kara da cewa kusa da cibiyar bayanan wani akwati ne mai dauke da na’urar karanta kati masu zabe amma gobarar bai shafe su ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *