fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Gobara Ta Kone Shaguna A Kasuwar Saida Kayyyakin Motoci ta Kaduna

Shaguna da dama a sanannen kasuwar kayayyakin mashin din hanyar Jos da ke yankin Oriapata a cikin jihar Kaduna gobara ta kone.

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar da ta fara da safiyar Juma’a ba, ‘yan kasuwa da mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa gobarar ta tashi ne daga daya daga cikin shagunan wanda kuma ke dauke da wasu’ yan haya a cikin gidan, sannan daga baya ya yadu zuwa shagunan kusa.
Shugabannin kungiyar dillalan kayayyakin motoci sun ce gobarar ta shafi ‘yan kasuwar da kayayyakinsu suka yi asara a gobarar.
Shugaban kungiyar dillalan kayan motoci na Kaduna, Cyprian Eneje, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta taimaka wa wadanda lamarin ya shafa domin basu damar fara rayuwa daidai.
A halin yanzu, jihar Kaduna da sauran sassan arewacin suna fuskantar mummunan yanayi saboda hunturu.
A wannan lokacin, al’amuran wutar galibi suna faruwa ne a kasuwanni ko kuma cikin gidaje.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *