fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Gobara ta lalata kayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Doya a yankin Filato

Kayayyakin abinci da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin nairori sun lalace sakamakon wata gobara da ta tashi a sanannen Kasuwar Doya ta Yamu a karamar hukumar Quaan Pan da ke jihar Filato a daren Lahadi.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Kabiri Buba, ya ce yawancin manoma da ‘yan kasuwa yanzu haka suna kirga asarar da suka yi.
Buba ya ce, “Manoma da ‘yan kasuwa sama da 100 matsalar ta shafa”.
Ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta taimaka wa manoma da ‘yan kasuwa.
Dangane da lamarin, Sanatan da ke wakiltar Filato ta Kudu, Nora Dadu’ut a ranar Litinin ya yi ta’aziyya tare da babban basaraken yankin, Long Jan na Namu mai martaba, Alhaji Safiyanu Allahnana da sauran al’ummar musamman wadanda abin ya shafa.
Dadu’ut ta ce ta yi bakin ciki game da lamarin.
“Ina jajantawa daukacin mutanen Namu kan wannan abin bakin ciki.
“Tunda na ji wannan lamarin, ban kasance kamar yadda na saba ba, ina bakin ciki sosai.
“Ina rokon Allah Ya farfado da ruhin wadanda wannan lamarin ya shafa.
Yan majalisar ta yi kira ga gwamnati da sauran ‘yan kasa masu hannu da shuni da su ba da tallafi ga wadanda abin ya shafa, don taimaka musu cikin hanzari daga bala’in.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *