fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Gudaji Kazaure ya Nemi Sulhu Da Gwamna Badaru Na Jihar Jigawa

Honarabul Gudaji Kazaure, dan Majalissar tarayya mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kazaure, Roni,Gwiwa da ‘Yan Kwashi, ya ziyarci Gwamnan Jihar Jigawa Alh Badaru Abubakar, domin fahintar juna kan sabanin da ya nemi shiga tsakanin shi da Gwamna, wanda ya kai ga har Hon Gudaji Kazaure, yake kalubalatar Gwamna Badaru a kafar sadarwa ta Facebook.

Wanda hakan ya kai da har jam’iyyar APC ta karamar Kazaure ta dakatar da shi daga jam’iyyar.

Bayan ziyarar ne Hon Gudaji Kazaure ya wallafar wannan sako ta shafinsa na Facebook “Alhamdulillah! mun samu zama da mai gidana mai girma Gwamna akan dan sabani da aka samu, wanda ya kawo cece-kuce har wasu suka samu dama domin su bata mana zumuncin mu na shekara ashirin, to Alhamdulillah mun zauna mun fahimci juna komai ya wuce”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *