fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Gwamna Bala Muhammad na Bauchi babban abin koyi ne a fannin shugabanci

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Wata kungiyar matasa mai rajin kare muradin mutanen yankin Arewa-maso-gabas ta ce ci gaban yankin ba zai yiwu ba sai an yi koyi da salon mulkin Gwamnan jihar Bauchi, Dokta Bala Mohammed( Kauran Bauchi).
Kungiyar wadda aka fi sani da Northeast Progressive Youth Assembly, ta ce yankin na Gabas-maso-yamma yana cikin matsi na tattalin arziki kuma wajibi ne a dauki matakan da suka dace, kwatankwacin matakan da Gwamna Bala Mohammed ya dauka don habaka fannin samun kudaden shiga.

A wata takardar da ya rattaba wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai, shugaban kungiyar, Salisu Tirmizi, ya ce wajibi ne sauran gwamnonin jahohin Gabas-maso-yamma su bude wani asusu don zuba naira biliyan biyar-biyar, da za a iya assasa babban bankin kasuwanci na bai-daya. Sanarwar, ta bayyana cewa muddin gwamnonin ba su yi hakan ba, to sauran bankunan kasuwanci guda 30, na ‘yan kudancin kasar nan za su ci gaba da mamaye ko’ina a yankin.
Kungiyar, ta ci gaba da jaddada cewa lokacin dogaro da kudaden shiga daga Gwamnatin Tarayya ya wuce, don haka wajibi ne gwamnonin su canza salo, su bi irin tsarin da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi yake aiwatarwa wajen samar da ababen more rayuwa ga jama’arsa.
Haka kuma, kungiyar ta ja kunnen gwamnonin jahohin na Gabas-maso-yamma da su dauki alkawarin kafa ma’aikatar wutar lantarki ta Mambila a matsayin ishara, ganin yadda al’amarin ya koma labarin kanzon kurege a yau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *