fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Gwamna El-Rufai ya nada dan shekara 28 a matsayin shugaban hukumar saka hannun jari ta jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasi El-Rufai ya nada Khalil Nur Khalil dan shekara 28 a matsayin babban sakataren hukumar bunkasa saka hannun jari ta Kaduna.

Wannan nadin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye.

Kafin sabon nadin nasa, Khalil ya kasance Darakta, Masanin kula da Zuba Jari a KADIPA, ya yi aiki da hukumar tun daga shekarar 2018.

Dangane da bayanin sa na LinkedIn, Khalil ya kammala karatun digiri na farko daga Jami’ar Gabashin Bahar Rum, Cyprus kuma yana da digiri na farko a fannin tattalin arziki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *